‘Yan Sama Jannatin Sin Sun Yi Nasarar Kammala Horon Farko Cikin Kogo
‘Yan sama jannatin kasar Sin su 28 sun yi nasarar kammala horon farko da aka shirya musu a cikin wani kogo na musamman dake yankin Wulong na birnin Chongqing.
Horon na kusan wata guda, wanda cibiyar bincike da horar da ‘yan sama jannatin ta Sin ke jagoranta da gudanarwa, ya tanadi darussa sama da goma, kamar na sa ido kan yanayi, da zana taswirar kogon, da kwaikwayon ayyukan sadarwa tsakanin sama da kasa, da horo game da halayen tunani na tawagar.
An ce, yanayin kogon yana kama da matsanancin yanayin sararin samaniya. Har ma dan sama jannati Ye Guangfu, wanda a shekarar 2016 ya taba halartar horon kogon gwajin a Turai, ya bayyana cewa, horon na wannan karo ya kunshi sabbin abubuwa a tsarin horar da ‘yan sama jannatin na Sin, ya kuma inganta cikakkiyar kwarewar ‘yan sama jannatin game da fuskantar matsanancin yanayi. Ya kuma bayar da goyon baya mai karfi ga ‘yan sama jannati na gaba wajen aiwatar da ayyuka na tsawon lokaci a cibiyar sararin samaniya da sauran ayyukan binciken duniyar wata. (Amina Xu)