Hare-haren ‘Yan Bindiga: An Sake Buɗe Makarantu A Kebbi Da Kwara
[ad_1]
Gwamnatocin jihohin Kebbi da Kwara sun sanar da sake buɗe makarantu a wasu yankuna, wanda hakan ke nuna ci gaba da gudanar harkokin ilimi a sannu-sannu bayan shafe watanni makarantun suna rufe sakamakon ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga a yankunan.
A Kebbi, gwamnatin jihar ta amince da sake buɗe wasu zaɓaɓɓun makarantun firamare da sakandare a manyan birane da garuruwa nan take.
- AFCON 2025: Morocco, Senegal Da Mali Sun Tsallaka Zuwa Zagayen Kwata Fainal
- Tinubu Ya Sha Alwashin Adalci Ga Waɗanda Aka Kashe A Kasuwar Neja
In ba a manta ba, jihar ta ba da umarnin rufe makarantu bayan harin ‘yan bindiga da aka kai a Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, garin Maga, ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a watan Nuwamba, inda aka sace ‘yan mata ‘yan makaranta 25 aka kuma kashe mai gadin makarantar.
Kwamishinar Ilimi Dr. Halimatu Bande, ta sanar da sake buɗe makarantun a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai a Birnin Kebbi.
A cewar Bande, komawa makarantun zai fara aiki daga Litinin, 5 ga Janairu, 2026, kuma ya shafi makarantu ne kawai dake cikin biranen jihar. Makarantun da ke yankunan karkara za a buɗe su daga baya, bayan an samu ƙarin ci gaba a fannin tsaro.
[ad_2]
Source link