Wanda ya kitsa harin bam a Masallacin Maiduguri ya shiga hannu




Dakarun Sojin Operation Haɗin Kai (OPHK) sun kama wanda ake zargi da jagoranci kai harin ƙunar baƙin wake a wani Masallaci da ke yankin Gamboru a birnin Maiduguri na Jihar Borno.

Sojojin sun sanar da hakan a ranar Juma’a, bayan wani binciken leƙen asiri da suka yi a yankin Kalmari na Maiduguri a ranar 31 ga watan Disamba, 2025.

A cewar sanarwar, an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a hare-haren bam na ƙunar baƙin wake.

Bincike ya nuna yadda ƙungiyarsu ke aiki, tsare-tsarenta da kuma alaƙar mambobinta.

Wani da ake zargi da kai harin bam, Ibrahim Muhammad, ya bayyana Shariff Umar a matsayin shugaban ƙungiyar tasu.

Ya ce Umar ne ke ɗaukar mutane, yana shirya su, sannan yana tura su inda za su kai hare-hare.

Sojojin sun ce bayanan da aka tabbatar sun nuna cewa Shariff Umar ne, ke tsara hare-hare da kuma samar da bama-bamai da ake amfani da su.

Bincike ya kuma nuna cewa Umar ne, ya shirya harin bam da aka kai a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga watan Disamba, 2025.

Haka kuma, an danganta Umar da yunƙurin kai wani harin bam a Damaturu, bayan da ya bai wa wanda zai kai harin kayan fashewa a Maiduguri.

Sojojin sun ce matar Umar, Yagana Modu, na da hannu a lamarin, yayin da ’yar uwarsa Amina ta ce ta ga wanda ya kai harin a gidansu kafin faruwar harin.

Sanarwar ta ce wannan bincike ya nuna yadda ’yan ta’adda da masu taimaka musu ke ɓuya a cikin al’umma.

A halin yanzu, duk waɗanda ake zargi suna hannun hukuma, kuma ana ci gaba da bincike don kama sauran masu hannu a harin.

Rundunar ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da jama’a, inda ta bayyana cewa ’yan ta’adda kan fak a cikin al’umma.

Ta buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro cikin gaggawa, domin taimakawa wajen hana hare-hare a yankin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *