An Koro Ƴan Nijeriya 366 Daga Kanada, Wasu 974 Na Fuskantar Korar
Hukumar kula da iyakokin Kanada (CBSA) ta kora ’yan Nijeriya 366 daga ƙasar tsakanin Janairu zuwa Oktoban 2025, yayin da matakan tilasta dokokin shige da fice suka kai matsayi mafi tsauri cikin fiye da shekaru goma. Bayanai sun kuma nuna cewa ’yan Nijeriya 974 na cikin jerin mutanen da ake shirin kora daga Kanada a halin yanzu.
Ƙididdigar, wadda aka sabunta a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ta nuna cewa Nijeriya ta zo ta tara a cikin ƙasashe 10 da aka fi korar ƴan ƙasarsu daga Kanada a wannan lokaci, yayin da ta zo ta biyar wajen yawan mutanen da ke fuskantar korar da ke ci gaba. Hakan na nuna ƙaruwar tsauraran matakai kan baƙin haure a ƙasar.
- Sin Ta Fitar Da Sakamakon Bincike Game Da Yadda Kanada Ke Nuna Wa Kayayyakinta Wariya
- NIS Ta Ƙaddamar Da Sabon Ingantaccen Fasfo A Ƙasar Kanada
Binciken bayanan ya nuna cewa adadin ƴan Nijeriya da ake korar su ya bambanta a tsawon shekaru. A 2019 an kori 339, adadin ya ragu zuwa 302 a 2020, 242 a 2021, sannan 199 a 2022. Bayan rashin bayyana a jerin manyan ƙasashe a 2023 da 2024, Nijeriya ta koma jerin a 2025 da mutane 366 cikin watanni 10, ƙarin kashi takwas cikin ɗari idan aka kwatanta da 2019.
Rahoton ya ce hakan na faruwa ne yayin da Kanada ke korar kusan baki 400 a kowane mako, inda a shekarar kasafin kuɗi ta 2024–2025 aka kori mutane 18,048 da kuɗin kusan dala miliyan 78.
Dokar shige da fice ta Kanada ta tanadi nau’o’in umarnin korar mutum uku—barin ƙasa cikin kwanaki 30, hana dawowa na tsawon lokaci, ko kuma korar dindindin—inda galibin waɗanda ake kora su ne ƴan neman mafaka da suka gaza cike ƙa’ida.