Cin amanar jama’a ne sauya sheƙar Mutfwang —PDP

[ad_1]



Jam’iyyar PDP reshen Jihar Filato ta nuna rashin jin daɗi kan sauya shekar da Gwamna Caleb Mutfwang, zuwa jam’iyyar APC, tana mai kiran hakan da cin amanar jama’a.

Kakakin PDP na jihar, Choji Felix Dalyop, ya tabbatar da cewa sun karɓi takardar murabus ɗin gwamnan ta hannun shugaban PDP na Mazaɓar Ampang West, Ƙaramar Hukumar Mangu.

A cewar Dalyop, “Aikin da Gwamna Mutfwang ya yi cin fuska ne ga mutanen Filato da suka ba shi amana duk da ƙalubale, kuma cin amanar akidar jam’iyya ne. Ya fifita son zuciya da burin kansa fiye da jin daɗin jama’ar Filato, kuma ba za a ɗauki wannan abin da wasa ba.”

Ya ce jam’iyyar ba ta taɓa samun shawara daga gwamnan kan batun sauya sheƙar ba, duk da jita-jitar da ake yaɗawa. Ya ƙara da cewa babu wani dalili na doka da zai halatta ficewarsa daga PDP zuwa APC ba tare da ya sauka daga kujerarsa ba.

“Wannan sauya sheka tamkar neman amfani da damar siyasa ne da ya take muradin jama’a, kuma neman amfanin kansa ne fiye da jin daɗin al’ummar Filato,” in ji shi.

Dalyop ya yi kira ga jama’ar jihar da su riƙa ɗaukar Mutfwang da alhakin wannan mataki, tare da ƙin amincewa da yunƙurinsa na neman sake tsayawa takara a sabuwar jam’iyya.

Ya kuma gargaɗi APC reshen Filato da kada ta rungumi Mutfwang hannu bibbiyu, domin hakan zai sa ta zama abokiyar cin amanar jama’a.

Sai dai ya shawarci mambobin PDP da magoya baya da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu juriya da tsayin daka, yana mai jaddada cewa PDP na nan daram, kuma za ta ci gaba da shiga dukkan zabubbukan da za su zo.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *