Jihar Neja Ta Buɗe Makarantu Bayan Ceto Ɗaliban Da Aka Sace

[ad_1]

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya amince da sake buɗe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar, bayan an ceto ɗalibai da ma’aikatan St. Mary Catholic School da aka sace a Papiri a ƙaramar hukumar Agwara. Wannan mataki ya biyo bayan rufe makarantu sakamakon lamarin satar mutane da ya tayar da hankula.

A wata sanarwa da Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare, Dr. Hadiza Asebe Mohammed, ta fitar, ta ce buɗe makarantu zai fara aiki ne daga ranar 12 ga Janairu, 2026. Ta bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan cikakken tantance tsaro da shawarwari da hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja
  • Yadda Takaddama Ta Kaure Bayan Ceto Daliban Neja 130

Ta ƙara da cewa duk da buɗe makarantu gaba ɗaya, makarantun da ke yankunan da har yanzu ake ganin ba su da isasshen tsaro ba za a buɗe su nan take ba. A cewarta, ana ci gaba da tantance dukkan makarantu domin tabbatar da lafiyar ɗalibai da malamai kafin ranar da aka tsara.

Gwamnatin jihar ta rufe makarantu ne tun bayan sace kimanin ɗalibai da ma’aikata 230 a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, lamarin da ya tilasta dakatar da jarrabawar zangon farko da kuma rufe manyan makarantu na ɗan lokaci. Gwamnati ta ce matakin buɗe makarantu na nuna ƙudurin ta na kare rayuka tare da tabbatar da ci gaban ilimi a jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *