Sin Ta Yi Allah Wadai Da Neman Ballewa Da Katsalandan Daga Waje Da Sunan Zaman Lafiya A Tsakanin Mashigin Taiwan

[ad_1]

A yau Jumma’a, wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasa ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta amince da duk wani yunkuri na dakile matakanta na yaki da neman ballewa, ko kuma katsalandan a cikin harkokin cikin gidanta ta hanyar amfani da hujjar tabbatar da zaman lafiya a fadin mashigin tekun Taiwan ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar Zhang Xiaogang, ya bayyana haka ne yayin da yake amsa wata tambayar ‘yan jarida game da kalaman da jagoran Taiwan Lai Ching-te da wasu kasashe da suka hada da Amurka, Japan, Australia da Philippines suka yi kan atisayen soja mai lakabin “Kudurin Adalci na shekarar 2025”, wanda rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) reshen gabashi ta gudanar kwanan nan.

Zhang ya ce Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da sauran yankunan kasar Sin ba, kuma batun Taiwan zallar al’amari ne na cikin gidan kasar Sin kawai, wanda bai shafi duk wani tsoma baki daga waje ba. Matakan da rundunar ‘yantar da jama’ar kasar Sin ta dauka na yaki da ‘yan aware da kuma shisshigin ‘yan katsalandan a kewayen Taiwan halal ne, da suka wajaba, kuma ba za a iya zargin lamarin ba. Babbar gaskiyar abin da yake na zahiri a Taiwan shi ne duka mashigin tekun Taiwan bangarori ne da suka kasance na kasar Sin daya tilo a duniya, kuma babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan ita ce ayyukan ‘yan aware na neman “‘yancin kan Taiwan” da kuma hadin baki da goyon bayan wasu daga waje. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *