Kakakin Babban Yankin Sin: Jawabin Jagoran Taiwan Lai Ching-Te Cike Yake Da Karairayi Da Nuna Kiyayya
[ad_1]
Mai magana da yawun babban yankin kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis cewa, jawabin sabuwar shekara da jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te ya gabatar cike yake da karairayi da nuna kiyayya, tare da neman tabbatar da tunani mara kan-gado game da “‘yancin kan Taiwan”, kana ya haddasa zaman dar-dar a fadin mashigin Taiwan.
Mai magana da yawun ofishin gwamnatin babban yankin Sin mai kula harkokin Taiwan Chen Binhua ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa, “Ko ma mene ne Lai da mahukuntan jam’iyyar Democrat Progressive Party suka ce ko suka yi, ba za su iya canza gaskiyar cewa Taiwan wani bangare ne na kasar Sin ba, kuma ba za su iya canza rugujewar da batun ‘yancin kan Taiwan’ zai yi ba makawa ba.”
Chen ya ce, “Tabbas za a cimma cikakkiyar nasarar sake hade kasar gado.”
Kazalika, ya ce, jawabin Lai ya bayyana matsayinsa na kafe kai da fata a kan “‘yancin kan Taiwan” da kuma tunaninsa na yin fito-na-fito, inda hakan ya fallasa ainihin yanayinsa na mai kawo cikas ga zaman lafiya, da tayar da husuma, da kuma haddasa yaki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link