Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Kira Taron Gaggawa Bayan Isra’ila Ta Amince Da ’Yancin Kan Yankin Somaliland

[ad_1]

Jiya Litinin, kwamitin sulhu na MDD ya kira taron gaggawa bisa rokon kasar Somaliya, inda aka tattauna kan batun amincewar da Isra’ila ta yi game da ’yancin kan yankin Somaliland. A yayin taron, bangarori da dama sun nuna adawa kan matakin da Isra’ila ta dauka, inda suka nuna cewa, matakin ya saba wa dokar kasa da kasa, tare da kalubalantar yanayin zaman lumana da zaman lafiya na yankin baki daya.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Sun Lei ya bayyana a yayin taron cewa, kasar Sin tana mai da matukar hankali kan yadda Isra’ila ta amince da ’yancin kan yankin Somaliland da kuma kafa dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu, tana kuma nuna adawa da hakan. Ya kuma jaddada cewa, mutunta ’yancin kan kasa da cikakken zamanta shi ne tushen kundin tsarin MDD, kana tushe na dokar kasa da kasa da ka’idar dangantakar kasa da kasa. Yankin Somaliland, wani yanki ne na kasar Somaliya, kasar Sin tana goyon bayan kasar Somaliya wajen kare ’yancin kai da dunkulewar kasa da kuma cikakken zamanta. Tana kuma nuna adawa da duk wani matakin da zai haddasa rabuwar kasar Somaliya.

Haka zalika, a madadin wasu kasashen Afirka da Latin Amurka na kwamitin sulhu na MDD, zaunannen wakilin kasar Somaliya a MDD Abkar Dahir Osman ya yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na amincewa da ’yancin kan yankin Somaliland. Yana mai cewa, wannan mataki ya keta ’yancin kan kasar Somaliya da cikakken zaman kasarta. (Mai Fassara: Maryam Yang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *