’Yansanda Sun Kama Masu Laifi 3,081 A Kano A 2025

[ad_1]

Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 3,081 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar a shekarar 2025.

Kwamishinan ’Yansanda na jihar, CP Ibrahim Bakori ne, ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar a hedikwatar ’yansandan da ke Bompai a Kano.

  • An Kashe Mutane 8 A Wasu Sabbin Hare-hare A Kebbi, ‘Yansanda Sun Fara Bincike
  • Kotu Ta Tisa Ƙeyar Malami Zuwa Gidan Yarin Kuje

Ya ce an yi kamen ne daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Disamba, 2025.

An gudanar da ayyukan kamen a sassan ’yansanda 78, rundunonin yankuna 11 da kuma sassan aiki na musamman guda bakwai.

Ayyukan sun haɗa da haɗin gwiwar sassan aiki, bincike da tattara bayanan sirri na rundunar.

A cewarsa, mafi yawan waɗanda aka kama ’yan daba ne.

An kama kimanin 2,350 bisa laifin tayar da hankalin jama’a, satar wayoyin hannu da makamantan laifuka, musamman a cikin birnin Kano.

Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da mutane 146 da ake zargi da fashi da makami, mutane 50 da ake zargi da garkuwa da mutane, mutane 112 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, mutane 85 da ake zargi da satar motoci, mutane 45 da ake zargi da satar adaidaita sahu, mutane 83 da ake zargi da satar babura, mutane 154 da ake zargi da sata, da kuma mutane 36 da ake zargi da damfara.

Kwamishinan ya ce an samu waɗannan nasarori ne bayan tantance matsalar tsaro da aka yi bayan shigar ofis a ranar 17 ga watan Maris, 2025.

Tantancewar ta nuna cewa barazanar tsaro a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar sun haɗa da harkar daba, shan miyagun ƙwayoyi, garkuwa da mutane, shigowar ’yan bindiga ta yankunan kan iyaka, da kuma rikicin manoma da makiyaya.

Ya ce rundunar ta ɗauki matakai daban-daban don magance matsalolin.

Matakan sun haɗa da aikin ’yansanda bisa bayanan sirri, ƙarfafa hulɗa da al’umma, haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro wajen sintiri a yankunan kan iyaka, horar da jami’ai, ƙarfafa sashen yaƙi da laifukan Intanet, da wayar da kan jama’a.

Bakori ya kuma ce aikin da aka ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” ya rage yawan faɗan daba da satar wayoyi.

Ya ƙara da cewa rundunar ta kuɓutar da mutane 14 da aka sace, tare da ƙwato bindigogi, makamai masu hatsari, miyagun ƙwayoyi, motocin sata da sauran kayayyakin laifi.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, shugabannin al’umma da kuma kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suka bayar.

Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da inganta waɗannan nasarori a shekarar 2026 ta hanyar ƙara sintiri, inganta tattara bayanan sirri da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da al’umma domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *