Pantami ya yi Allah-wadai da kisan masallata a Katsina

[ad_1]



Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi Allah-wadai da kisan masallata da ’yan bindiga suka yi a wani masallaci da ke Malumfashi, a Jihar Katsina.

Harin ya faru ne a ranar Talata lokacin da mutane ke sallar Asubah, inda aka kashe aƙalla mutane 27, sannan aka jikkata wasu da dama.

Shugabannin al’umma da jami’an asibiti ne suka tabbatar da harin.

Farfesa Pantami, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar Unguwan Mantau da kuma ɗaukacin mutanen Katsina.

Ya bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki “sun fi dabbobi muni,” domin sun kashe mutane ne a yayin suke ibada.

Ya buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki mataki mai tsauri kan ’yan ta’addan, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano su.

A cewarsa, jami’an tsaro na iya amfani da bayanan wayar hannu, hasashen hasumiyoyin sadarwa, da tsarin GPS don gano masu laifin.

Ya ce ya daɗe yana bayar da wannan shawara tsawon shekaru shida da suka wuce.

Pantami, ya yi addu’a Allah Ya karɓi shahadar waɗanda aka kashe, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri da juriya.

Haka kuma ya yi addu’ar zaman lafiya da tsaro a Najeriya baki ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *