Sin Za Ta Kyautata Tsarin Lura Da Kudin Kasar Na Dijital A Shekara Mai Kamawa

[ad_1]

A yau Litinin ne babban bankin kasar Sin PBOC, ya sanar da shirinsa na daga darajar tsarin lura da kudin kasar yuan na dijital, inda ingantaccen tsarin hakan zai fara aiki tun daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2026 dake daf da shigowa. Karkashin tsarin ingantaccen kudin na “digital yuan”, kudin zai zarta kamanceceniya da kudin takarda kadai, inda zai zamo kudin dijital da za a iya ajiyarsa bankuna.

Tsarin zai kuma kunshi sabon mazinin awo, da na gudanarwa, da tsarin hada-hada da na tabbatar da nasarar cudanya da kudin, kamar dai yadda babban bankin na kasar Sin ya bayyana.

Sauyin da kudin na dijital na Sin zai fuskanta, zai kasance ci gaba da gwajin da ake yi kan sa, a kasuwannin cikin gida da na tsallake, wanda hakan ya kai shi ga samun matukar karbuwa a sassan amfanin yau da kullum masu tarin yawa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *