Harin Bam A Masallacin Borno Aiki Ne Na Rashin Imani — Ministan Sufuri


Ministan Sufuri, Sanata Said Ahmed Alkali, ya yi Allah-wadai da harin bam da ya auku a Masallacin Juma’a na Al-Adum, da ke yankin Kasuwar Gamboru, a birnin Maiduguri na jihar Borno, inda ya bayyana lamarin a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Umar Alkali Jibril, ya fitar, Alkali ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Borno kan lamarin yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.

  • Mutane 5 Sun Rasu, 35 Sun Jikkata A Harin Bam A Masallaci A Borno
  • Mutane Da Dama Sun Rasu Bayan Tashin Bam A Masallaci A Borno

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan rayukan waɗanda suka rasu, Ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

Rahoton farko daga Rundunar Ƴansandan Jihar Borno, ya bayyana cewa mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu 35 suka samu munanan raunuka sakamakon harin.

Jaridar SHUGABANCI ta ruwaito cewa waɗanda suka jikkata suna karɓar kulawar lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, da kuma Asibitin Ƙwararru na Jihar Borno, da ke Maiduguri, babban birnin jihar.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *