Majalisar Wakilai ta umurci a sake wallafa sabbin dokokin haraji

[ad_1]



Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin sake fitar da manyan dokokin sauye-sauyen haraji guda huɗu, bayan cece-kuce a bainar jama’a kan zargin yin cushe cikin abin da ta amince da shi.

Majalisar ta jaddada cewa matakin na gudanarwa ne kawai domin kare mutunci da martabar dokokinta.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Akin Rotimi, ya fitar a ranar Juma’a, y ace jagorancin majalisar biyu ta umarci Akawun Majalisar da ya sake fitar da dokokin tare da bayar da kwafin da majalisun suka amince da shi a matsayin kwafi na asali

Umarnin ya biyo bayan ƙara yawan muhawara a bainar jama’a kan yadda aka amince da dokokin, shugaban ƙasa ya rattaba hannu a kansu kuma wallafa su a cikin kundin dokokin kasar.

A cewar Majalisar, damuwar da aka bayyana ta shafi “daidaita dokokin da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka amince da su, takardun da aka tura don rattaba hannu na shugaban ƙasa, da kuma nau’o’in dokokin da daga baya aka wallafa.

Rotimi ya ce majalisar tana gudanar da lamarin cikin bin kundin tsarin mulki.

“Majalisar Wakilai na tabbatar wa jama’a cewa ana yunkurin magance waɗannan batutuwa cikin tsanaki bisa bin kundin tsarin mulki da dokokin da suka shafi Majalisar Ƙasa,” in ji shi.

Ya ce makon da ya gabata, majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi mai mutum bakwai bayan an yi korafi a kan zargin yin cushe a dokar a zauren majalisa.

Sanarwar ta ce, “Kwamitin tare da sauran kwamitocin da suka dace na Majalisar, suna aiki tare da shugabancin majalisar wajen gudanar da binciken cikin gida domin gano jerin abubuwan da suka faru da kuma gano duk wani abu da ya haifar da halin da ake ciki kan yadda aka gudanar da dokokin.”

Rotimi ya ƙara da cewa binciken zai haɗa da “bin kwakkwafi kan duk wata kura, rashin daidaito, ko tsoma baki daga waje idan aka tabbatar da su,” yana mai jaddada cewa ana gudanar da aikin bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ma dokokin majalisar.

Ya ce jagorancin Majalisar Dokokin ƙarƙashin Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da ta Wakilai Abbas Tajudeen, sun bayar da umarnin sake fitar da dokokin domin kawar da duk wani ruɗani ko shakku a zukatan ’yan kasa.

“Wannan matakin gudanarwa na nufin tabbatar da sahihanci da kuma nuna ainihin abin da majalisar ta amince da shi,” in ji sanarwar.

Sai dai sanarwar ta jaddada cewa wannan sake nazarin ba yana nufin amincewa da wani kuskure a cikin dokokin ba ne.

Majalisar ta kuma yi kira ga jama’a da su yi haƙuri, tana mai cewa za a ci gaba da bayar da ƙarin bayani yayin da binciken ke tafiya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *