Najeriya Na Da Wata Kawa Mai Sanin Ya Kamata
[ad_1]
Kowa na son hulda da abokai masu sanin ya kamata, saboda suna girmama mutane, da saukin kai, kuma za a iya dogoro a kansu. Hakika hulda a tsakanin kasashe ma kamar haka take, inda kasa mai sanin ya kamata za ta yi kokarin kyautata hulda da sauran kasashe, don tabbatar da ci gaba mai dorewa ga juna. Kuma tabbas ba za ta dauki matakai irinsu kara harajin kwastam, da kin yarda da shigowar mutanen sauran kasashe cikin harabarta, da barazanar daukar matakin soja, da wata kasa ta kan dauka ba, wadanda ke ta da hankalin mutanen duniya a-kai-a-kai.
Sai dai wani abu mai kyau shi ne, ganin yadda kasar Najeriya ta samu wata kawa mai sanin ya kamata, wato kasar ta Sin. Idan mun waiwayi ayyukan hadin gwiwa da kasashen Najeriya da Sin suka yi a shekarar 2025 da muke ciki, to, za mu ga yadda aka samu dimbin sakamako:
An ce, darajar cinikin da aka yi tsakanin Najeriya da Sin, tun daga watan Janairu zuwa na Oktoban bana, ta riga ta kai dalar Amurka biliyan 22.3, jamillar da ta karu da kaso 30.2% bisa na makamancin lokacin bara. Kana duk a cikin wannan wa’adi, kudin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a kasar Najeriya kai-tsaye ya karu da kaso 130%, kana kudin kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa kasar Sin ya karu da fiye da kaso 200%, a kan na makamancin lokacin bara.
Sa’an nan, a wajen bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka da ya gudana da watan Yunin bana, a birnin Changsha na Sin, gami da taron baje kolin kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin daga ketare, da aka shirya a birnin Shanghai na kasar Sin, a watan Nuwamban bana, duk an gayyaci Najeriya ta halarta a matsayin babbar bakuwa, inda ta samu damar nuna wa mutanen duniya nasarorin da ta samu ta fuskar raya kasa, da kayayyakin musamman da ta samar, gami da shigar da amfanin gonarta irinsu yazawa, da ridi, da gero, da citta cikin kasuwannin kasar Sin.
Haka zalika, ana amfani da dimbin kayayyakin more rayuwa da Najeriya da Sin suka gina a hadin gwiwarsu yadda ake bukata. Misali, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu ta tashar jiragen ruwa ta Lekki dake jihar Lagos ya karu da fiye da kashi 82% a bana, bisa jimillar ta shekarar bara. Kana yawan fasinjoji da kayayyakin da aka kwashe ta layin dogon da ya hada Lagos da Ibadan, da karamin jirgin kasa dake tafiya a cikin birnin Lagos, dukkansu sun nuna bajinta mai tarihi, a sa’i daya kuma ana kokarin gudanar da wasu sabbin ayyukan hadin gwiwa na gina kayayyakin more rayuwa, irinsu “birnin tattalin arziki” na Ajaokuta dake jihar Kogi, da yankin sarrafa iskar gas na Ogidigbon dake jihar Delta, da dai sauransu.
To, watakila masu karanta wannan bayani za ku yi tambaya cewa, me ya sa kasar Sin ta iya zama wata kawa mai sanin ya kamata? Dangane da tambayar, za mu iya samun amsa daga cikin wani bayanin da Stephen Ndegwa, wani shahararren masanin ilimin siyasa na kasar Kenya, ya rubuta a kwanan baya.
Cikin bayaninsa mai taken “Mece ce ma’anar tsarin zamanantarwar kasar Sin ga kasashe masu tasowa?” da gidan rediyon Capital FM na kasar Kenya ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, Mista Ndegwa ya ce, “ Tsarin Sin na zamanantarwa ya dora muhimmanci kan huldar abota da hadin gwiwa, maimakon tsarin nuna bambanci, da dogaro kan wani.” A ganinsa, dalilin da ya sa kasar Sin ta zame wa sauran kasashe kawa mai sanin ya kamata, shi ne domin yadda kasar ta fahimci hakikanin yanayin da duniyarmu ke ciki. Wannan yanayi shi ne, don raya tattalin arziki, ana bukatar hada masana’antu, da hanyoyin jigilar kayayyaki, da makamashi, da kasuwanni, da sauran fannoni waje guda. Kana wannan hadewa za ta haifar da ci gaba na bai-daya na kasashe daban daban, wadanda ake samun daidaito da hadin kai a tsakaninsu.
Mista Ndegwa ya kara da cewa, a ganin kasar Sin, ci gaban wata kasa ba ya nufin cin moriya da faduwar wata. Akasin haka, ci gaban wani ya kan zama tushen ci gaban saura. Saboda ci gaban kasashe masu tasowa ya kan haifar da karin bukatu a kasuwannin duniya, da rage yiwuwar abkuwar rikici, da kuma karfafa tsarin samar da kayayyaki. A cewar Ndegwa, wannan ra’ayi ya sa kasar Sin kara kokarin goyon bayan hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tawowa, inda take mika wa sauran kasashe fasahohi, da samar da damammaki na samun horo, da ba da rance a kokarin tallafa wa kokarin sauran kasashe na raya kasa, da dai sauransu.
Hakika ra’ayin da Mista Ndegwa ya ambata shi ne ra’ayin “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya” da kasar Sin ke kokarin yayatawa a duniya. A bisa ra’ayin, ya kamata duk wata kasa ta lura da bukatun sauran kasashe, yayin da take neman tabbatar da moriyar kanta, da kokarin cimma burin samun ci gaba na bai-daya na kasashe daban daban. A wannan zamanin da ake kara fama da ra’ayi na kariyar ciniki da daukar mataki na kashin kai, a zahiri ne, ra’ayin Sin ya nuna mana wata alkibla da ta dace, ta tabbatar da daidaito, da adalci, gami da walwala a duniya. (Bello Wang)
[ad_2]
Source link