Ba Zan Goyi Bayan Tinubu A 2027 Kamar Wike Ba — Makinde
Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba.
Ya kuma ce Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi alƙawarin taimaka wa Tinubu ta fuskar siyasa ba tare da tuntuɓar jam’iyyar PDP ba.
- ‘Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Fashi A Kano
- ’Yan Ta’adda Ba Su Da Mafaka A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin jihar da ke Ibadan.
Ya ce saɓaninsa da Wike na siyasa ne, ba na ƙashin kai ba, kuma ya bayyana matsayarsa ƙarara game da zaɓen 2027.
“Ina da zaɓina na kaina, kuma ba zan goyi bayan Shugaba Tinubu a 2027 ba,” in ji Makinde.
Gwamnan ya ce rikicin ya fara ne a wani taro da Shugaba Tinubu, Wike da sauran manyan jami’ai suka halarta, inda Wike ya yi wata magana da ta ba shi mamaki game da makomar jam’iyyar PDP.
“Wike ya faɗa wa shugaban ƙasa cewa zai riƙe PDP dominsa a 2027. Na yi matuƙar mamaki, domin ba mu taɓa cimma matsaya a kan hakan ba,” in ji Makinde.