Mangal ya dauki nauyin tiyatar masu cutar yoyon fitsari 100 a Katsina

[ad_1]



Marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi sama da 100 ne suka amfana da  tiyata kyauta daga tallafin tiyatar cutar yoyon fitsari kyauta daga shahararren ɗan kasuwa a Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal na shekara-shekara, a wannan karon.

Aminiya ta ruwaito cewa an gudanar da aikin ne a Asibitin Kashi ta Amadi Rimi da ke yankin Karamar Hukumar Batagarawa, inda ba ’yan Katsina kaɗai suka amfana ba, har ma da marasa lafiya daga jihohin makwabta.

Malam Hussaini, ɗaya daga cikin mambobin kwamitin da ke kula da aikin, ya bayyana cewa wannan aikin na cikin jerin ayyukan jinƙai da Alhaji Mangal ke ɗaukar nauyi a duk shekara, musamman a irin waɗannan lokutan.

Waɗanda aka yi wa tiyata sun nuna farin cikinsu tare da godiya ga Allah da kuma jinjina wa Alhaji Mangal bisa ɗaukar nauyin aikin. Sun kuma yi kira ga masu hali da su rika taimaka wa marasa ƙarfi ta fannoni daban-daban.

Ɗaya daga cikin wadanda suka amfana, Malam Dauda Waziri, ya ce zuciyarsa ta cika da farin ciki, domin ya daɗe yana fama da cutar fitsari amma bai samu damar yin tiyata ba saboda rashin kuɗi.

Shi ma Malam Ibrahim Lawal ya bayyana cewa ya fi shekaru uku yana rayuwa da cutar, amma tsadar aikin da rashin kuɗi ya hana shi samun magani.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *