’Yan Bindiga Sun Sace Matafiya 28 A Jihar Filato
[ad_1]
’Yan bindiga sun sace aƙalla matafiya 28 a daren ranar Lahadi a ƙauyen Zak da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Wani shugaban matasa, Sapi’i Sambo, ya ce waɗanda aka sace sun haɗa da maza, mata da yara.
- An Bullo Da Sabon Daftarin Dokar Kiyaye Muhallin Halittu Na Kasar Sin
- AFCON 2025: Afirka Ta Kudu Ta Doke Angola Da Ci 2-1
Suna kan hanyarsu ne daga Zak zuwa Sabon Layi domin halartar bikin Mauludi lokacin da aka kai musu hari da misalin ƙarfe 8 na dare.
Ya ce maharan sun tare motar sannan suka tafi da dukkanin fasinjojin, suka bar motar a wajen.
Daga cikin waɗanda aka sace akwai ’ya’yan masu sauratar gargajiya biyu da kuma wani malamin addini.
An gano motar da aka bari da safiyar ranar Litinin, amma har yanzu ba a san inda aka kai mutanen ba.
An sanar da jami’an tsaro game da lamarin.
’Yansanda sun ce suna binciken faruwar lamarin.
Sace-sace da ayyukan ’yan bindiga sun yi ƙamari a yankin Wase.
[ad_2]
Source link