Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda
Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu garkuwa da mutane da kungiyoyi masu daukar makamai da masu tayar da hankali a matsayin ’yan ta’adda, a wani mataki da aka bayyana a matsayin sabon salo na yaki da satar mutane, hare-hare kan manoma da tashin hankali a cikin al’umma.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyaan wa taron manema labarai na ƙarshen shekara a Abuja cewa wannan mataki ya kawo ƙarshen rudani kan matsayin irin waɗannan laifuka, inda yanzu za a yi mu’amala da su a matsayin ta’addanci.
“Daga yau duk wata ƙungiya ko mutum da ya yi garkuwa da ’ya’yanmu, ya kai hari ga manomanmu, ko ya tsoratar da al’ummarmu, za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda kuma za a yi mu’amala da shi a haka,” in ji Idris. “Lokacin yin amfani da sunaye marasa tabbas ya ƙare.”
Ya bayyana cewa wannan manufa za ta ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, wanda zai ba da damar saurin ɗaukar mataki.
Ya kuma nuna nasarorin da aka samu a bana, ciki har da kama manyan laifuka da aka fi nema a duniya ta hanyar haɗin gwiwa.
Domin kare yankunan karkara, Idris ya sanar da tura masu gadin daji da aka horar da su tare da kayan aikin sa ido da saurin ɗaukar mataki.
Ana sa ran waɗannan jami’an za su katse hanyoyin samar da kayan abinci ga ’yan ta’adda, rushe maboyarsu, tare da ba da kwarin gwiwa ga manoma da ke fama da rashin tsaro.
Gwamnati ta ce wannan mataki na nuna rashin sassauci ga masu garkuwa da mutane da tashin hankali a karkara.
Idris ya kuma bayyana kama shugaban ISWAP da ke zaune a Najeriya, wanda ke cikin ’yan ta’adda mafi nema a Afirka, wanda Amurka ta sanya lada mai tsoka a kansa. Ya kuma tuna da kama Abu Barra a watannin baya.
“A halin yanzu wannan mutum tare da shugaban ma’aikatansa suna fuskantar shari’a, kuma za su samu hukuncin da ya dace da su,” in ji Idris.
Wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnati na ɗaukar garkuwa da mutane da tashin hankali a karkara a matsayin ta’addanci, ba kawai laifukan da aka saba ba.