An Rubuta Sabon Babi Kan Yin Kirkire-kirkiren Fasahohin Zamani A Yankin Kogin Yangtse Delta Na Kasar Sin

[ad_1]

Bayan da aka gudanar da taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 18, birnin Shanghai ya yi kokarin taka muhimmiyar rawa wajen yin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, da jagoranci aikin raya karfin yin kirkire-kirkire a yankin kogin Yangtse Delta, da raya kungiyar hadin gwiwar raya fasahohin zamani, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin Sin yadda ya kamata, da kuma samun ci gaba mai inganci.

A halin yanzu, ana samu kamfani mai shiga kasuwar hannun jari guda daya a kowane muraba’in kilomita na unguwar raya fasahohin zamani ta Zhangjiang dake birnin Shanghai, rabin manyan kamfanonin samar da magunguna na duniya 20 suna kafa cibiyoyin bude kofa da yin kirkire-kirkirensu a Zhangjiang, kana akwai kashi 40 cikin dari na manyan kamfanonin masana’antun samar da magunguna na kasar Sin a wurin. Yawan manyan ayyukan more rayuwa na fasahohin zamani da aka gama ginawa, da wadanda ake ginawa da kuma wadanda ake shirin ginawa a birnin Shanghai ya kai 20. Adadin kamfanonin fasahohin zamani a birnin ya zarce dubu 25, adadin kwararru a fannonin da suka shafi manyan fasahohin zamani kamar hadaddiyar hanyar sarrafa lantarki, da magunguna na zamani, da fasahar AI a wurin ya zarce dubu 800.

Bisa jagorancin birnin Shanghai, ana kokarin yin kirkire-kirkiren fasahohin zamani a yankin kogin Yangtse Delta gaba daya. Unguwar Zhangjiang ta birnin Shanghai da birnin Hefei na lardin Anhui wato manyan cibiyoyin kimiyya da fasaha na kasar Sin suna kokarin sa kaimi ga yin hadin gwiwa da juna, da musayar manyan na’urorin fasahohin zamani dubu 56 a tsakanin yankuna, kana cibiyar kirkire-kirkiren fasahohin zamani ta yankin kogin Yangtse Delta ta yi hadin gwiwa tare da kwalejojin nazarin kimiyya da fasaha da jami’o’in kasar Sin da na kasashen waje, da kuma kafa cibiyoyin hadin gwiwa ta yin kirkire-kirkire tare da manyan kamfanoni kimanin 600. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *