Sin Ta Nuna Adawa Da Kalaman Jami’in Japan Game Da Mallakar Makaman Nukiliya

[ad_1]

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Litinin cewa, wajibi ne kasashen duniya su sa-ido sosai tare da nuna adawa da kalaman wani babban jami’in kasar Japan na cewa, ya kamata kasar ta mallaki makaman nukiliya.

Lin ya bayyana cewa, a bana aka cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin kasar Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. Sojojin kasar Japan sun kaddamar da yaki na zalunci tare da aikata miyagun laifuka na rashin imani, inda suka kirkiro da shafi mafi duhu a tarihin dan Adam.

Kazalika, ya ce, duk da shan kaye da ta yi, Japan ba ta taba cikakkiyar kawar da ummul-haba’isin amfani da karfin soja a kasar ba. Wasu masu fada a ji da ke cikin Japan ba wai kawai sun kasa yin tunani kan tarihin zaluncin Japan ba ne, har ma sun nuna matukar rashin jin dadi game da tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin. Idan aka saki mara ga masu ra’ayin rikau na Japan suka kera rantsattsun makamai, ko kuma suka mallaki makaman nukiliya, hakan zai sake haddasa masifa a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *