Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

[ad_1]


Wata mummunar gobara ta lalata Kasuwar kayan ɗaki ta Sabuwar Lale da ke Tal’udu, ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, inda ta ƙone shaguna da dama tare da jefa ’yan kasuwa cikin jimami. Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 2:30 na asubahin Lahadi, ta kuma bazu cikin sauri kafin jami’an kashe gobara su iso.

Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar da abin ya shafa, Bashir Ustaz, ya ce ya gigice matuƙa bayan ya isa kasuwa ya tarar da shagonsa ya ƙone ƙurmus. “Da misalin ƙarfe 3 na dare aka kira ni aka ce gobara ta tashi. Da na zo, abin da na gani ya sa na rufe idona. Duk abin da na mallaka gobara ta cinye,” in ji shi, ya ƙara da cewa kasuwar cike take maƙil da harkar kasuwanci kwana guda kafin faruwar lamarin.

Mataimakin Shugaban Kasuwar, Adamu Mansur wanda aka fi sani da Madaki, ya ce gobarar ta ci gaba da ruruwa tun daga ƙarfe 2:30 na dare har zuwa wayewar gari. Ya ce har yanzu ba a tantance jimillar asarar ba, amma wasu shaguna sun yi asarar kayan ɗaki na miliyoyin naira. “A shagona kaɗai ina da kayan ɗaki sama da guda 40 da zan kai yau; huɗu daga ciki sun kai fiye da Naira miliyan 5, wasu kuma sama da miliyan 4,” in ji shi.

Rahotanni sun nuna cewa a ƙalla shaguna 11 da kuma kusan rumfunan wucin gadi 20 ne suka ƙone ƙurmus. Jami’an kashe gobara sun shafe sa’o’i suna fafutuka kafin su shawo kan gobarar bayan sallar asuba, duk da cewa babu asarar rai da aka samu.

Ƴan kasuwar sun ce gobarar ta katse musu babban tushen samun abin dogara, inda Madaki ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da masu hannu da shuni da su tallafa musu bisa asarar da suka yi. Jaridar Daily Trust ya rawaito cewa, har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan musabbabin gobarar ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *