An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
[ad_1]
Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun shiga fargaba, bayan wasu da ba a san ko su waye ba, suka kashe wata mai ciki da ɗanta ɗan wata18 a duniya.
An tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da mijin matar ya dawo gida daga aiki ya tarar ƙofar gidan a kulle.
A cewar maƙwabtan matar, bayan mijin ya tambayi jama’a a unguwar, sai ya shiga gidan, inda ya tarar da gawar matarsa da ta ɗanta.
Daga nan ne al’ummar unguwar suka sanar da hukumomin tsaro.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban jama’a aunguwar, Ahmad Sani, ya ce jama’a sun shiga firgici da tashin hankali matuƙa.
Ya koka da rashin tsaro a yankin, inda ya bayyana cewa duk da gina ofishin ’yan sanda a unguwar, har yanzu ba a turo jami’an tsaro da za su kula da shi ba.
“Dukkanin al’ummar unguwar sun shiga ruɗani. Ba a taɓa samun irin wannan abu ba. Muna cikin damuwa saboda babu jami’an tsaro a nan,” in ji shi.
Ya roƙi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, da ya ɗauki matakin gaggawa wajen inganta tsaro a yankin domin hana sake faruwar hakan.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba zai ce komai ba domin rundunar na gudanar da bincike.
A halin yanzu, mazauna yankin sun buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata laifin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link