Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Samar Da Damammakin Raya Tattalin Arziki Ga Duniya A Shekara Mai Zuwa

[ad_1]


Shugaban asusun hadin gwiwar kasar Amurka da kasar Sin John Milligan-Whyte, ya zanta da kafar CMG a kwanan nan, inda ya tabo batun taron da shugabannin kasar Sin suka gudanar a kwanan baya, kan aikin raya tattalin arzikin kasar, yana mai cewa a lokacin da ake kara fuskantar yanayin rashin tabbas a fannin raya tattalin arzikin duniya, kasar Sin ta gabatar da ingantattun manufofi na daidaita yanayin tattalin arzikin cikin gidanta, lamarin da zai haifar da damammakin samun ci gaba ga sauran kasashe.

A halin yanzu, ra’ayin kariyar ciniki ya sake fara yaduwa a duniya, kana tashe-tashen hankali na faruwa a kai a kai, saboda haka, kasashe daban daban suna matukar bukatar damar sa kaimi ga bunkasar tattalin arziki. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta dade tana samar da wani yanayi mai kwantar da hankalin al’ummun duniya, ta hanyar goyon bayan yunkurin raya tattalin arzikin kasashe daban daban.

A kwanan baya, dimbin kungiyoyin hada-hadar kudi, da suka hada da Asusun Lamuni na Duniya (IMF), da Bankin Duniya, da dai sauransu, sun daga mizanin saurin karuwar tattalin arziki, da suke hasashen kasar Sin za ta samu. Kazalika, a yanzu haka kasashe daban daban suna jiran samun kwarin gwiwa da damammaki, bisa yanayin aiwatar da tsare-tsaren raya tattalin arziki na shekara mai zuwa a kasar Sin.

A wajen taron tsara ayyukan raya tattalin arziki da shugabannin kasar Sin suka gudanar a wannan karo, an tabbatar da niyyar kasar ta kara inganta tsarin tattalin arziki, da daukar manufar hada-hadar kudi mai yakini, don daidaita wasu matsalolin da aka taba fuskantar a baya, da neman cika burikan da aka sanya a gaba.

A ganin Malama Zhang Monan, wata masaniyar ilimin tattalin arziki ta kasar Sin, sakonnin da taron tattalin arzikin na wannan karo ya gabatarwa duniya, za su kwantar da hankalin ‘yan kasuwa masu zuba jari na kasashe daban daban, ganin yadda suka shaida cewa, yanayin karuwar tattalin arzikin Sin cikin dogon lokaci bai canza ba. Kana ingancin tsare-tsare, da saurin karuwa mai kima na tattalin arzikin Sin, za su haifar da karin damammakin bunkasa tattalin arziki ga kasashe daban daban. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *