Rikicin PDP Ne Ya Sanya Ni Komawa Jam’iyyar Accord

[ad_1]


Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce bai bar jam’iyyar PDP haka kawai ba, yana da dalilan da ya sa shi ficewa daga jam’iyyar.

Ya ce rikicin jam’iyyar ne ya tilasta masa komawa jam’iyyar Accord domin sake neman wa’adi na biyu a 2026.

Adeleke, yayin da yake magana da gidan talabijin na Channels, ya ce yana ƙauanar PDP kuma ya yi ƙoƙari sosai wajen magance matsalolin jam’iyyar, amma rikicin sai ƙaruwa yake yi kullum.

Ya ce shiga jam’iyyar Accord ya zama dole ne domin kare kansa, kula da ci gaban jihar, da kuma samun ingantaccen wajen da zai tsaya takarar 2026.

Ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa mutanen Osun za su zaɓe shi saboda aikinsa, ba saboda jam’iyya ba.

Adeleke ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar Accord tun ranar 6 ga watan Nuwamba, 2025, bayan shawarwari da tattaunawa da manyan jiga-jigai.

Kwana guda bayan ya bayyana sauyawa jam’iyya, Accord ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamnanta na 2026.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *