Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso

[ad_1]



Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya aike wasiƙar neman shiga wata jam’iyya ta daban.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce babu gaskiya a labaran, kuma ya shawarci jama’a da su yi watsi da su.

“Mun samu bayanin wasu rubuce-rubucen da ke yawo a Intanet cewa mun miƙa wasiƙar neman shiga wata jam’iyya a ƙasar nan.

“Muna so mu fayyace wa jama’a cewa ba mu taɓa miƙa irin wannan wasiƙa ga kowace jam’iyya ba.

“Saboda haka mun shawarci jama’a da su riƙa neman duk wani bayani game da mu daga shafukanmu na gaskiya,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ta hasashen komawar Kwankwaso jam’iyyaar APC kafin zaɓen 2027.

Aminiya ta ruwaito cewa akwai alamun cewa Kwankwaso ya tattauna da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan yiwuwar komawa jam’iyyar mai mulki.

Majiyoyi daga APC a Jihar Kano, sun yi iƙirarin cewa Kwankwaso ya aike wa sakatariyar jam’iyyar a Abuja wasiƙa, inda ya bayyana ƙudirinsa na sake shiga jam’iyyar.

Amma Aminiya ba ta tabbatar da wannan batu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Sai dai wata majiya daga sakatariyar APC a Abuja, ta ce Kwankwaso da shugaban jam’iyyar na ƙasa sun daɗe suna tattaunawa kan shirin sauya sheƙarsa, kuma shirye-shiryen sun yi nisa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *