Bom ya kashe yara 2 wasu 6 sun jikkata a Borno

[ad_1]



Fashewar bom ta kashe yara biyu tare da jikkata wasu shida a yankin Kofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi guda bisa rashin sani.

“ Tabbas yara biyu sun mutu nan take, bayan sun kawo bom ɗin gida a matsayin ƙarfen gwangwan bisa rashin sanin haɗarinsa,” a cewar wani mazaunin garin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *