Ba Mu Da Hujjar Juyawa Gwamna Uba Sani Da Tinubu Baya — Tsohon Gwamnan Kaduna

[ad_1]


Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Dakta Mukhtar Ramalan Yero, (Dallatun Zazzau) ya bayyana cewa al’ummar jihar Kaduna basu da wata hujja ko dalilin da zai sa su yi watsi da Gwamna Uba Sani ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zabukan da ke tafe.

Dakta Ramalan Yero, ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da shugabannin kungiyar ‘Uba Sani Alheri Ne‘ ta jihar Kaduna karkashin jagorancin Dakta Bashir Idris Lifidan Jama’a Wanda ya gudana a dakin taro na Arewa House.

Dallatun Zazzau, ya ce shugabancin Uba Sani da na Tinubu ya nuna kwararan hujjoji na jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma, samar da tsaro da kuma aiwatar da manufofi masu amfani ga kasa da jihohi.

Ya bayyana cewa a jihar Kaduna, gwamnan Uba Sani ya nuna kwarewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati cikin natsuwa, sauƙaƙe rayuwa ga talakawa, da kuma rungumar tsarin mulki mai mutunta ‘yancin jama’a. Ya kara da cewa, sauye-sauyen da ake gani a fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro da harkokin noman sun sa jama’a da dama suka fara ganin sauyi a zahiri a wurare daban-daban a fadin jihar.

Game da gwamnatin tarayya kuwa, tsohon gwamnan ya ce, Shugaba Tinubu ya fara aiwatar da nau’ikan gyare-gyare masu tsauri, wadanda za su bukaci hakuri da fahimtar jama’a, tare da tabbatar da cewa tsarin tattalin arziki da manufofin kasa suna samun karbuwa a duniya.

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci ‘yan siyasa da su kauce wa yada maganganu marasa tushe, su mayar da hankali kan gaskiya da neman mafita ga matsalolin jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *