’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa

[ad_1]



An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa.

Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan.

Sanarwar rundunar ’yan sanda ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa jami’an tsaro da ke gadin gidan sun yi ƙoƙarin dakile harin, inda aka samu musayar wuta.

A yayin arangamar, biyu daga cikin jami’an sun samu munanan raunuka, aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Washegari, ɗaya daga cikin waɗanda suka ji rauni ya rasu a sakamakon tsananin raunukan da ya samu.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, Ɗahiru Muhammad, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da abokan aikinsa, yana mai tabbatar da cewa rundunar ta fara bincike na musamman domin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.

Bayan harin, rundunar ta ƙara tsaurara matakan tsaro ta hanyar yawaita sintiri da sanya ido a Aujara da maƙwabtan garuruwan domin hana sake faruwar irin wannan barazana.

Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya roƙi al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka wa binciken da ake yi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *