Sojoji Sun Ceto ‘Yan Mata 12 Da Boko Haram/ISWAP Suka Sace A Borno
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce dakarunta na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai ta Arewa maso Gabas sun yi nasarar ceto ‘yan mata 12 da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar a shafukanta na sada zumunta, ta ce an sace ‘yan matan ne, wadanda shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 20, a ranar 23 ga Nuwamba yayin da suke girbin amfanin gona amma an ceto su a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, 2025.
A cewar sanarwar, an ceto ‘yan matan ne bayan wani samamen gaggawa da kwarewa da jami’an tsaro suka yi a yankin kudancin Borno.
An kwashe ‘yan matan da aka ceto zuwa wani sansanin soja mai tsaro inda suke samun kulawar lafiya.