Hanyoyi Biyar Da Za Mu Bi Domin Inganta Fatar Jikinmu
[ad_1]
Yana da kyau mace ta kasance mai yawan gyaran jiki a koyaushe.
Musamman idan ita matar aure ce, kuma ga lokaci kamar yanzu na sanyi fata na yawan bushewa. Sau da yawa sai a ga mace daga ta haihu daya ta fita daga kammaninta. Idan mace ta kasance mai yawan gyara, a kullum maigida zai rika yi mata kallon kamar budurwa. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin inganta fatar jiki.
1. Idan ana so fatar jiki ta kasance da santsi a kullum, za a iya hada man zaitun da gishirin teku (sea salt); za a iya samun wannan gishirin a manyan shagunan da ake sayar da kayan kwalliya. Idan aka kwaba su sai a rika dirzawa a jiki a kullum kafin a shiga wanka. Yin haka na cire matacciyar fatar da ke jiki kuma ya fitar da sabo. Bayan haka, ga sanya fata santsi da laushi.
2. Idan ana yawan shafe-shafe, kuma fatar ta yi wani dabbare-dabbare, sai a samu lemun zaki ko na tsami ana goge inda wannan fatar ta canja launi. Sai a jira na tsawon minti hudu sannan a wanke. Yin haka na haskaka wannan wurin da ya kode a fatar.
3. Man Tuffa na daya daga cikin abubuwan da ke gyara fatar kai. Kuma yana warkar da kowace irin cuta ta fatar kai. A samu man tuffa kamar kofi daya sai a hada da ruwa sannan a wanke kan da shi duk lokacin da kan ya yi datti. Yawan amfani da man tuffa na rage fitowar amosanin kai da kurajen kai.
4. Zuma za a same ta a ko’ina. Tana dauke da sinadarai da dama kamar na sanya santsin fata da kuma warkar da tabo da sauransu. A shafa zuma a fuska a kullum kafin a shiga wanka, sannan a bari ta dan jima na minti goma ko fiye da haka sai a wanke da ruwan dumi. Yin haka na warkar da kurajen fuska da sanya ta haske da santsi.
5. A kasance ana da man kwakwa a kullum domin wannan mai na gyara fatar kai da kuma sanya gashi laushi da santsi da kuma tsawo. A shafa man kwakwa a fatar kai sannan a rufe kan da leda, bayan awa daya sai a wanke za a yi mamaki.
[ad_2]
Source link