Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku

[ad_1]



Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su.

Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar APC da PDP, yanzu ya fahimci cewa ba za su kawo wa ƙasar nan mafita ta matsalolin da ake fuskanta.

A makon da ya gabata ne Atiku ya karɓi katin zama mamba na ADC, abin da ya tabbatar da shigarsa jam’iyyar a hukumance.

Ya yi kira ga jama’ar Taraba, musamman mata da matasa, su shiga ADC domin, a cewarsa, jam’iyyar za ta taimaka wajen inganta tsaro da farfado da tattalin arzikin Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *