Furucin Takaichi Game Da Taiwan Ya Aike Da Mummunan Sako Ga ’Yan Awaren Yankin
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce, kalaman da firaministar kasar Japan Sanae Takaichi ta yi game da yankin Taiwan na kasar Sin, ya aike da mummunan sako ga ’yan awaren yankin. Haka kuma, ma’aikatar ta soki jagoran yankin Taiwan din Lai Ching-te game da yadda ya nuna goyon-baya ga Japan.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana hakan a yau Jumma’a, inda ta ce kalaman firaminista Takaichi, wadanda suka yi nuni da yuwuwar amfani da makamai a Zirin Taiwan, sun jawo suka da adawa daga kasa da kasa da ma mutanen da suka san ya kamata a cikin Japan. Sai dai, Lai Ching-te ya wallafa wani hoto a shafinsa na sada zumunta yana dauke da Sushi, wani nau’in abincin kasar Japan da ake yi da abincin teku, domin nuna goyon-baya ga Japan din.
Mao Ning ta ce, Japan ta yi mulkin mallaka a Taiwan na tsawon rabin karni, kuma ta aikata munanan laifuka da dama a wurin. Tana mai bayyana yunkurin hukumomin jam’iyyar DPP na jan ra’ayin Japan domin ta goyi bayan ballewar yankin, a matsayin raini.
Mao ta bukaci Japan ta yi nazari mai zurfi kan laifukan da ta aikata a tarihi, ta dauki darasi daga tarihi kuma ta rungumi manufar Sin daya tilo a duniya da yin taka-tsantsan wajen furta kalamai da aiwatar da abubuwan da suka shafi batun Taiwan. (FMM)