An Jinjinawa Dabarun Kasar Sin Na Ci Gaban Noma Da Ciniki Mai Dorewa
[ad_1]
A yayin taron na 114 na kwamitin noma na kungiyar ciniki ta duniya (WTO), wanda aka gudanar daga ranar 24 zuwa 26 ga watan nan, kasar Sin ta shirya wani taro mai taken “Ci gaban noma da ciniki mai dorewa,” inda ta raba dabaru da tsare-tsarenta, wanda hakan ya samu yabo daga dukkan mahalarta taron.
Babban jami’in ofinshin cinikayya na kasar Sin a WTO Qin Tianfang, ya bayyana cewa, a halin yanzu, tsarin noma da ciniki na duniya na fuskantar sauye-sauye, yayin da sauyin yanayi, tashin hankali a fagen siyasa, da tasirin cutar COVID-19 suka raunata tsarin samar da abinci a duniya, wanda ke kawo hadari mai tsayi ga burin samar da isashen abinci a duniya. Kalubalen da ake fuskanta a ci gaban mai dorewa na bukatar hadin gwiwar kasa da kasa.
Yawancin wakilan da suka halarci taron sun yi imanin cewa, a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, dabaru da tsare-tsaren kasar Sin na ci gaban noma da ciniki mai dorewa na da amfani ga kasashe masu tasowa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link