Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina.

Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida.

Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba.

Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a minti na 3, sai Olakunle Alaka ya kara ta biyu a minti na 30.
A daidai minti na 45, kafin a je hutun rabin lokaci, Joseph Arumala ya rage tazara ga Ikorodu City.

Duk da wannan nasarar, Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na 20, inda take da maki 9 a ƙasan teburin gasar.

A wani labarin, ƙungiyar Katsina United ta samu nasarar doke Enyimba da ci 3–2 a birnin Ilorin, inda take buga wasanninta na gida bayan dakatar da ita daga yin wasa a filin gidan ta a Katsina.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *