Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta




Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Santa Maria da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar.

Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a.

Shugaban Sashen bayar da Agaji na Ƙaramar Hukumar, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula, amma bai bayar da cikakkun bayani ba.

Sai dai a cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Abubakar Usman, ya ce bayan samun bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a yankin.

Sai dai ya  ce makarantar da abin ya shafa ta ƙi bin umarnin ta kuma buɗe makarantar.

“Gwamnatin Jihar Neja ta yi matuƙar bakin ciki da labarin sace ɗaliban makarantar St. Mary da ke Ƙaramar Hukumar Agwara. Har yanzu ba a tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace ba yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tantance lamarin.

“Jihar ta samu bayanan sirri tun da farko da ya nuna ƙaruwa barazanar tsaro a wasu sassan yankin arewa.”

“A kan haka ne Gwamnatin jiha ta bayar da umarnin dakatar da dukkan ayyukan gine-gine tare da rufe dukkan makarantun kwana a yankin da abin ya shafa a matsayin kandagarki

“Sai dai makarantar St. Mary ta ci gaba da zama a buɗe da ci gaba da karatu ba tare da sanarwa ko neman izini daga gwamnati ba.”

“Jami’an tsaro sun riga sun fara cikakken bincike da aikin ceto domin tabbatar da an dawo da ɗaliban gida lafiya.”

“Gwamnatin Jihar Neja tana aiki kai tsaye da dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa kuma za ta ci gaba da bayar da rahotanni yayin da bayani kara fitowa.”

“Gwamnati na kira ga masu makarantu, shugabannin al’umma, da duk masu ruwa da tsaki da su bi ƙa’idojin tsaro da aka bayar domin kare rayukan jama’a. Kariya ga rayuka, musamman na ’ya’yanmu, ita ce babban abin da wannan gwamnatin ta sa a gaba,” in ji shi.

A Jihar Kwara makwabciyar Nejan, gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantu fiye da 50 a kananan hukumomi hudu sakamakon sake ƙaruwar hare-hare a yankunansu.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *