Jihar Kwara Ta Rufe Makarantu A Ƙananan Hukumomi 4

[ad_1]


Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a kananan hukumomi hudu na Jihar a daidai lokacin da ake fama da rashin tsaro a wasu al’ummomin jihar.

Ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT), reshen Jihar Kwara ce, ta bayyana sanarwar a madadin gwamnati a ranar Laraba.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba kuma LEADERSHIP ta samu, shugaban NUT, Yusuf Agboola, ya sanar da rufe makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun, da Ekiti.

‎Agboola ya bayyana cewa, matakin ya biyo bayan umarni mai tsauri daga Ma’aikatar Ilimi da Ci gaban Jama’a bayan da gwamnati ta nuna damuwa game da sabbin barazanar tsaro a yankin Kudancin Kwara.

In ba a manta ba, LEADERSHIP Hausa ta rahoto cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kan reshen Cocin Christ Apostolic (CAC) a Oke Isegun a cikin al’ummar Eruku, karamar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara a ranar Talata, 18 ga Nuwamba, 2025, inda suka kashe akalla masu ibada biyu tare da sace sama da mutane 35, ciki har da faston cocin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *