Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai
Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.
Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU.
Aminiyar ta ruwaito cewa, ɗaliban sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyar a jami’o’in Bayero da kuma North West —Mudassir Adamu Musa da Asahabulkhair Labaran Usman —suka jagoranta.
Ɗaliban sun bayyana cewa yajin aikin da ƙungiyar ASUU ke shiga lokaci zuwa lokaci a dalilin taƙaddama da gwamnati yana gurgunta makomar karatunsu da kuma ilimi a ƙasar baki ɗaya.
Ƙungiyar ɗaliban ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da cika duk wata yarjejeniyar da ta ƙulla da ASUU, tana mai cewa muddin aka samu wani abu akasin haka, to babu shakka lamarin zai ci gaba da kawo tasgaro a harkokin ilimi a faɗin ƙasar.
Ɗaliban sun tunatar da duk masu ruwa da tsakin cewa ba su halin karatu a jami’o’in masu zaman kansa ballantana fita neman ilimi a ƙasashen ƙetare irin su Birtaniya, Indiya ko Amurka kamar yadda suke gani ’ya’yan masu hannu da shuni suna yi.