An Bude Dandalin Tattauna Hadin Gwiwar Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Tsakanin Sin Da Afirka Na 2025

[ad_1]


A yau Alhamis ne aka bude dandalin tattauna hadin gwiwar kirkire-kirkire da ci gaba tsakanin Sin da kasashen Afirka na shekarar 2025 a birnin Wuhan na lardin Hubei. Ma’aikatar harkokin kimiyya da fasaha ta Sin, da gwamnatin jama’ar lardin Hubei ne suka dauki nauyin shiryawa dandalin.

A wannan karo, dandalin ya gudana ne bisa jigon “Samun sabbin damammakin hadin gwiwar kirkire-kirkire, da cimma zamanantarwa tare”, inda aka mayar da hankali kan fannoni kamar na hadin gwiwar masana’antu, da kirkire-kirkiren kimmiya da fasaha, da musayar al’adu, da aikin noma na zamani, da kiwon lafiyar jama’a, da ci gaba mai kiyaye muhalli.

A daya bangaren karkashin dandalin, an gudanar wasu taruka, da zaman tattaunawa, da taron gabatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da dandalin tattauna hadin gwiwar kimiyya da fasaha na cibiyoyin bincike na Sin da Afirka, da sauran taruka na musamman guda 12.

Kimanin baki 800, ciki har da manyan ‘yan siyasa, da jami’an diflomasiyya daga kasashe da yankuna 42 na Sin, da nahiyoyin Afirka, da Amurka da Turai, da kuma fitattun masana kimiyya, da masana masana’antu na Sin da Afirka sun halarci dandalin.

Ban da haka, bikin bude dandalin ya kunshi gudanar da bikin bayar da kyaututtukan lashe zangon karshe, na gasar kirkire-kirkire da kasuwanci ta matasa, tsakanin Sin da Afirka karo na 4. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *