A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci
[ad_1]
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen dake yammacin Afrika ta bukaci da a fita daga tsohon tsarin da ake bi wajen koyarwa a makarantun allo da na islamiyyu, a wani mataki na dakile karuwar ayyukan `yan ta`adda a shiyyar.
Wata sanarwa da ta fito jiya Juma`a daga sashen yada labarai na hedkwatar kungiyar da ke Abuja, ta ambato cewa shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Dr. Omar Touray ne ya bukaci hakan a karshen babban taron Musulunci da aka gudanar a kan tsaro da shugabanci wanda aka gudanar ranar Alhamis a birnin Abuja.
Taken taron dai shi ne rawar da kungiyoyin addinin Musulunci za su taka wajen yaki da hare-haren ta`addanci da sauran ayyukan `yan ta`adda a yammacin Afrika da yankin Sahel.
Shugaban hukumar gudanarwar ta ECOWAS ya ce zamanantar da irin wadannan makarantu da su kansu malaman makarantun zai taimaka sosai wajen kawo karshen matsalolin barace-barace a kan tituna da cin zarafin kananan yara da sauya tunanin kananan yara, wadanda daga nan ne aka ja su cikin kungiyoyin `yan ta`adda.
Ya ce batun tsarin koyarwa a makarantun allo shi ne batun da babban taron ya fi bai wa fifiko, inda ya ce kungiyar ta ECOWAS tana son a mayar da irin wadannan makarantu zuwa cibiyoyin zamani da za a rika koyar da ilimin addini da kuma na koyon sana’o’in dogaro da kai.
“A shekaru goma da suka gabata, ayyukan ta`addanci da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra`ayi ya haifar da mummunan koma bayan tattalin arziki da na zamantakewar alummomin dake shiyyar, halin da daliban irin wadannan makarantu suke ciki yana bukatar kulawar gaggawa daga kungiyar ta ECOWAS, abin takaici irin wadannan makarantun allo suna daukar dalibai masu yawan gaske kuma akasari kananan yara daga shiyyar, to amma kuma ba a bai wa makarantun da daliban kulawar da ta kamata, wannan ta sanya kungiyoyin `yan ta`adda ke samun kofar kusantar su domin kwadaita musu shiga cikin kungiyoyin.”
[ad_2]
Source link