Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA




Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labaru, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a muƙamin a watan Janairun 2021, bayan ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi daga shekarar 2018 zuwa Disamba 2020.

Sabon nadin na nufin tsohon hafsan soja dan asalin jihar Adamawa zai ci gaba da rike mukamin har zuwa shekarar 2031.

Marwa, wanda ya taba zama gwamnan soja na jihohin Legas da Borno, ya kammala karatu a Makarantar Soja ta Najeriya da kuma Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA).

Bayan ya zama cikakken soja a shekarar 1973, Marwa ya yi aiki a matsayin babban jami’in 23 Armoured Brigade, ya kasance babban dogari ga tsohon Babban Hafsan Soja, Laftanar-Janar Theophilus Danjuma, sannan ya yi aiki a matsayin Magatakardar Kwalejin Tsaro ta Najeriya.

Haka kuma ya yi aiki a matsayin Mataimakin Mashawarci kan Tsaro a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Washington DC, daga baya kuma ya zama Mashawarci kan Tsaro a Ofishin Jakadan Najeriya na Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.

Zaman Marwa a NDLEA ya yi fice wajen kama masu fataucin miyagun kwayoyi, inda aka cafke sama da mutane 73,000 da ke harkar fatauci da kuma kwace fiye da tan miliyan 15 na miyagun kwayoyi iri-iri.

A karkashin jagorancinsa, hukumar ta kaddamar da gangamin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a faɗin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya ce: “Sake nadinka alamar amincewa ce da kokarinka na kawar da kasar nan daga annobar fatauci da shan miyagun kwayoyi. Ina rokonka kada ka yi kasa a gwiwa wajen bin diddigin ’yan kasuwar miyagun kwayoyi da ke neman lalata al’ummarmu, musamman matasa.”




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *