Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
[ad_1]
A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.
Wannan wasan dai shi ne zai tabbatar da nasarar Nijeriya na samun tikitin shiga gasar kafin haɗuwar ta da Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Congo a ranar Lahadi.
Wasan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan tawagar Super Eagles da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) sun warware matsalolin da suka shafi kuɗaɗe tsakanin ‘yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa.
Kyaftin William Troost-Ekong ya tabbatar da cewa an biya dukkan haƙƙoƙin da suke bi, inda ya ce tawagar ta koma fili cikin karsashi da ƙwarin gwiwar neman nasara a wasan yau.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link