LABARAN SAFIYAR JUMAA 08-08-2025



Labaran Safiyar Juma’a 08/08/2025CE – 14/02/1447AH Ga Takaitattun Labaran.

Madugun adawa Atiku Abubakar ya buƙaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sanda.

Tsoffin Kansilolin APC a Kano sun yi zanga-zangar nesanta kansu da maganganun Abdullahi Abbas.

Gwamna Bago na jihar Neja yace sulhu da ƴan bindiga a jihohi makwabta, ya kara ta’azzarar rashin ysaro a jihar sa.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da shirin tattara ayyukan da za a saka a kasafin kuɗin jihar na 2026.

Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana.

Kauyuka 30 sun yi zanga-zanga kan ta’addancin ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti.

Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohin Arewa da Abuja ranar Juma’a, tana gargadin mazauna su dauki matakan kariya.

Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin jiya Alhamis.

’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama.

Al’ummar yankin Danjibga dake karamar hukumar Tsafe ta jihar na neman agajin gaggawa daga mahukunta sakamakon kawanya da yan bindiga suka yiwa garin.

Mutum 50 sun ɓace bayan afkuwar ambaliya a Indiya.

Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idriss Déby Itno ya kammala ziyarar wuni biyu da ya kai birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Lebanon ta ce harin Isra’ila ya kashe mutum biyar a ƙasar.

Barcelona ta yube Ter Stergen daga mukaminsa na kaftin din kungiyar.

AC Milan na son ɗauko Hojlund daga Manchester United. Darajar ɗanwasan ta kai fam miliyan 30 amma Milan na son aro ne.

Bayern Munich ta tuntuɓi Chelsea kan Nicolas Jackson, wanda Chelsea ke son fam miliyan 48, kuma Newcastle United na farautarsa.

Harin Isra’ila ya kashe ɗan kwallon Falasɗinawa Suleiman al-Obeid.

Sources
1. Hausaforum.com.ng
2. Aminiya.
3. BBC Hausa.
4. Leadership Hausa.
5. Legit Hausa.

source

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *