An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno
[ad_1]
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno.
A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya.
Sojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin Sashe na 2 na OPHK sun yi artabu da mayakan Boko Haram da ISWAP a Dutsen Kura, inda suka fatattake su bayan fafatawar da ta gudana har zuwa yankin Mangari.
Sanarwar ta bayyana cewa an gano mafakar ’yan ta’adda guda 11, sannan an kubutar da maza, mata da yara 86 da aka garkuwa da su.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 73, jigidar harsashi 5, motoci 5, babura 5, kekuna 8 da kuma babura masu ƙafa uku guda 2.
A wani samame na daban a Mangada, dakarun sun kama mutum 29 da ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kayayyaki, tare da kwace motocin ɗaukar kaya guda 2 da babura masu ƙafa uku cike da man fetur da man injin sama da lita 1,000.
Laftanar Kanar Uba ya ce an gudanar da duka ayyukan ba tare da asarar rai ko rauni a ɓangaren sojoji ba, inda babban kwamandan rundunar ya yabawa jarumtar dakarun tare da buƙatar su ci gaba da hana ’yan ta’adda samun damar shakatawa a duk faɗin yankin Arewa maso Gabas.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link