Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu.

Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa.

“Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin, inda ya ƙara da cewa an riga an kama wasu, kuma kotu za ta hukunta masu laifi.

Ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 150 ga iyalan waɗanda lamarin abin ya shafa a ƙauyukan Fulani, Zabarmawa da Arewa.

“Babu wani dalili da zai sa rikici ya shiga tsakaninsu, tun da kun shafe sama da shekaru 100 kuna rayuwa tare cikin zaman lafiya,” in ji shi.

Gwamnan, ya kuma yi alƙawarin neman taimakon Gwamnatin Tarayya domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa, tare da yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *