Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano




Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Abba ya yi wannan yabo ne, yayin da yake karɓar babban kwamandan rundunar soji ta 1, a Hedikwatar Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, a fadar gwamnati da ke Kano.

Manjo Janar Wase, ya ziyarci Kano domin duba halin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.

Ya bayyana yadda mahaifinsa, marigayi Kanal Muhammad Abdullahi Wase, ya taɓa zama kwamishinan soja na Jihar Kano a shekarar 1994.

“Tun lokacin da na karɓi jagorancin rundunar, na ziyarci wuraren da aka kai hare-hare domin na yaba wa jarumtar sojojimmu,” in ji Janar Wase.

Gwamnan ya gode wa sojoji bisa jajircewarsu, tare da jinjina wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan naɗa sabbin hafsoshin tsaro masu ƙwazo da kishin ƙasa.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda 10 da babura 60 ga rundunar haɗin gwiwa da ke aiki a yankunan da abin ya shafa.

Haka kuma ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu.

Idan ba a manta Aminiya ta ruwaito yadda dakarun soji suka daƙile hari tare da kashe ’yan bindiga 19 a yankin Shanono yayin wani samame da suka kai.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *