Ta yi garkuwa da kanta don karbar kuɗin fansa daga hannun mijinta
Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗin fansa daga mijinta.
An kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin, wato Martins Chidozie mai shekaru 23 da Osita Godfrey mai shekaru 33.
Mataimakiyar Kakakin rundunar a jihar, ASP Eno Ikoedem, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan bincike kan wani rahoton garkuwa da aka kai wa ’yan sanda.
Ta ce a ranar 27 ga Oktoba, 2025, wani mutum mai suna Paul Adaniken ya kai rahoto a ofishin ’yan sanda na New Etete cewa ya bar matarsa, Chioma Success Ezebie, da ɗansu mai shekaru uku, Andrea Ojiezelabor, a gida kafin ya tafi shagonsa.
A cewarta, daga bisani an kira shi da wata lamba da bai sani ba, ana sanar da shi cewa an yi garkuwa da matarsa da ɗansa.
Mai magana da yawun rundunar ta ce masu garkuwa sun nemi a biya su kuɗin fansa naira miliyan 5 kafin su sako su.
Ta ce yayin bincike, an gano cewa ɗan uwanta, Osita Godfrey, wanda a baya ake zaton yana taimakawa da bayani, shi ma yana da hannu a cikin laifin, kuma an kama shi.
Ta ƙara da cewa bayanin da Godfrey ya bayar ya kai ga kama Chioma Success, wadda ta haɗa baki da abokan aikinta don ƙitsa garkuwa da kanta da nufin karɓar kuɗi daga mijinta.
Ta ce an kuma kama wani da ake zargi, Martins Chidozie, dangane da laifin.
ASP Eno Ikoedem ta tabbatar da cewa an kwato kuɗin fansar da aka biya na naira miliyan biyar, kuma yanzu haka an mika batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar (SCID) domin ci gaba da bincike da gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.