Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Sojojin Nijeriya sun cafke ƴan ta’adda 20, sun kuma ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su a jerin hare-hare da binciken leƙen asiri da suka gudanar a sassa daban-daban. Haka kuma, sun gano wuraren tace haramtaccen Mai a yankin Kudu maso Kudu.
Wata majiyar daga shalƙwatar rundunar Sojin ta bayyana cewa ƴan ta’adda uku — Fannami Ari (Abu Dujana), da Hussaini Hassan Modu (Abu Yusuf) da wani mai koyon ta’addanci — sun miƙa wuya ga Sojoji a ƙananan hukumomin Kukawa da Damboa na Jihar Borno, bayan sun gaji da zaluncin shugabanninsu da tsananin rayuwa a sansanoninsu.
A yankin Arewa maso Gabas, Sojojin bataliya ta 192 tare da CJTF sun yi artabu da mayaƙan ISWAP da Boko Haram (JAS) a ƙauyen Hudugum na ƙaramar hukumar Gwoza, inda suka kashe ƴan ta’adda biyu. A Arewa maso Yamma kuwa, Sojojin Birgediya ta 1 sun daƙile sace mutane a Zamfara, inda suka ceto mutane 11 a yankunan Magami–Jan Gemi da Kucheri–Bilbis.
A Arewa ta Tsakiya, Sojojin Operation Enduring Peace (OPEP) da Operation Whirl Stroke (OPWS) sun gudanar da hare-hare a jihohin Filato, da Benue, da Nasarawa da Kaduna, inda suka kama mutane 15 da ake zargi da laifukan ta’addanci, da satar shanu da rikice-rikicen ƙabilanci, tare da ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da su a Filato da Taraba.
Haka kuma, a Kudu maso Kudu, Sojojin Bataliya ta 29 sun lalata karatun tace haramtaccen Mai guda biyu a yankin Biseni na Jihar Bayelsa, yayin da Birgediya ta 34 ta kama ganguna 62 na man fetur da aka sace — kimanin lita 3,000 a Ohaji/Egbema na Jihar Imo, domin daƙile aiyukan masu satar mai.