Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
[ad_1]
A karon farko, kasar Sin ta bayar da gudunmuwar sama da rabin muhimman makaloli na duniya, inda ta dauki kaso 53.2 na jimilar, kana ta rike matsayinta dake kan gaba a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani rahoto game da makalolin kimiyya na Sin na 2025 da cibiyar nazarin kimiyya da fasahar sadarwa ta Sin ko ISTIC ta fitar.
Muhimman makalolin na nufin wadanda aka wallafa cikin shekaru 2 da suka gabata, kuma suka samu adadi mai yawa na wadanda suka kafa hujja da su a wannan lokacin, lamarin da ya kai su cikin kaso 0.1 dake kan gaba a fanninsu, ta fuskar yawan kafa hujja da aka yi da su.
Zuwa watan Agustan 2025, irin wadannan makaloli na Sin sun kai 2,342, adadin da ya karu da kaso 4.6 kan na 2024, yayin da Amurka ke bi mata baya da guda 1,511. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
[ad_2]
Source link