COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa
Sabon Babban Hafsan Sojan Kasa (COAS), Manjo Janar Waidi Shaibu, ya yi alƙawarin cewa, Rundunar Sojin Nijeriya za ta yi aiki da ƙwarewa wurin murƙushe sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa, wacce ke da alhakin kai hare-hare a sassan arewacin Nijeriya.
Janar Shaibu, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin Babban Hafsan Soja a makon da ya gabata, ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya bayyana a Majalisar Dattawa don tantancewa a ranar Laraba, inda ya yi cikakken bayani game da gogewarsa ta soja kuma ya bayyana manyan manufofinsa na dawo da tsaro a faɗin ƙasar.
“Rundunar Sojan Kasa za ta yi aiki da kwarewa wurin murƙushe sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda da aka fi sani da Lakurawa cikin nasara,” in ji shi.
COAS Shaibu ya tabbatar wa ‘yan majalisar cewa, a ƙarƙashin jagorancinsa, sojoji za su ƙara himma wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da kuma ‘yan fashi da makami.
Da yake tunawa da gogewarsa a fagen daga, COAS Shaibu ya kara da cewa, ya taka muhimmiyar rawa a ayyukan yaki da ta’addanci a Jihar Borno, inda ya taimaka wajen samun nasarori masu yawa a kan ‘yan ta’addan Boko Haram.